Rahotanni

‘yan Bindiga sun kashe mutun takwas 8 da ‘yan Sanda uku 3 A jihar Zamfara.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin’ yan fashi ne a ranar Alhamis sun yi wa ayarin motocin Manjo Sanusi Muhammad Asha, Sarkin Kaura Namoda da ke Jihar Zamfara kwantan bauna, inda suka kashe mutane takwas, ciki har da ’yan sanda uku.
Majiyarmu ta saharaReporters sun gano cewa lamarin ya faru ne akan babbar hanyar Gusau-Funtua.
Bayanai sun ce Sarkin na kan hanyarsa ta zuwa wani aiki ne a Gusau lokacin da ’yan bindigar suka far wa ayarin motocinsa, inda suka kashe’ yan sanda uku.

An kuma kashe wani direban motar Hilux a cikin ayarin motocin, wani babban mai gadin masarautar da kuma wani Dan Amal, wanda kawun Sarki ne.

An Kira Mohammed Shehu, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ta Zamfara Amma ba a dauka ba kuma Bai Kira ba Zuwa yanzu .

Zamfara, kamar sauran jihohi a fadin arewa, tana shan fama da hare-haren yan fashi da masu satar mutane wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane da yawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button