Labarai

‘Yan bindiga sun kashe mutun uku sun Kuma sace mutun bakwai a Karamar Hukumar birnin Gwari Dake Jihar Kaduna.

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane uku a ranar Talata a wani hari da suka kai wasu kauyuka a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Mutane biyu ne suka mutu a lokacin da maharan suka kai hari a wata unguwa da ke kusa da unguwar Tanko Dogon Sarki da ke karkashin mazabar Kakangi a karamar hukumar Birnin Gwari da misalin karfe 9:00 na safe, kamar yadda mazauna garin suka bayyana.

‘Yan bindigar sun kuma kai hari kauyen Rafin Gora mai tazarar kilomita biyu daga yankin Dogon Dawa na mazabar da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar, inda suka kashe wani dan kauyen tare da yin awon gaba da wasu bakwai.

Wani dan kungiyar masu ci gaba da masarautar Birnin Gwari, wanda ya gwammace a sakaya sunansa saboda ba shi da izinin yin magana, ya tabbatar da faruwar lamarin Anguwar Tanko Dogon Sarki.

Ya kuma kara da cewa a wannan rana ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wasu mutanen kauyen a kauyen Tashar Keji da ke karkashin mazabar Kakangi a karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kakangi a majalisar dokokin jihar Yahaya Musa Dan Salio ya tabbatar da faruwar lamarin a kauyen Rafin Gora sai dai ya ce har yanzu bai samu cikakken bayani kan sauran abubuwan da suka faru ba.

Kiran da aka yi wa jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansur Hassan, bai amsa kiran ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button