‘Yan bindiga Sun Kashe Sarkin Tauri, Sun Sace Mutane A Katsina.
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani mutum mai suna Ashiru Aliyu mai shekaru 50 da safiyar ranar Litinin a Kauyen Daulai da ke karkashin karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
A cewar Jaridar Katsina Post, ta rawaito cewa;- ‘yan bindigar sun sace mata da yawa, wadanda kuma suka yi awon gaba da wasu dabbobin gida tare da wawushe kayan abinci a yayin harin.
An ce ‘yan bindigar sun isa kauyen da misalin karfe 1:00 na dare inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.
Hakanan, wadanda ake zargin ‘yan fashin sun kashe mai rike da sarautar gargajiya na Sarkin Tauri na garin Dandume sannan suka yi garkuwa da wasu mutane hudu ciki har da matan aure.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na Daren Jiya Litinin 14 ga watan Satumba, a cewar jaridar.
Daya daga cikin mazauna yankin ya ce ‘yan bindigar sun kai kimanin 30.
An kuma gano cewa wasu daga cikin mazauna kauyen sun tsere zuwa cikin daji da kuma garuruwan da ke kusa da su don kaucewa afka musu.
Ahmed T. Adam Bagas