Tsaro
‘Yan bindiga sun kashe Shugaban PDP a Katsina
‘Yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Sabuwa na jihar Katsina, Alhaji Lawal Dako.
Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party Sabuwa LGA Alhaji Lawal Dako wanda yan fashin suka harbe a ranar 8/11/2020 ya mutu a jiya Juma’a 20/11/2020 daga raunukan da suka samu sakamakon hare-haren.
Ya mutu a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello.