Labarai

‘Yan Bindiga sun kashe Sojoji biyu a wajen binciken Kan hanya Checkpoint a jihar Kogi.

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga a ranar Laraba da yamma sun kai hari a shingen binciken sojoji a karamar hukumar Okene ta jihar Kogi, inda suka kashe jami’ai biyu na rundunar sojojin ruwan Najeriya.

Jaridar Tribune Online ta aminta da cewa an kaiwa jami’an rundunar sojan ruwa hari da misalin karfe 7 na yammacin ranar Laraba a shingen binciken da ke Okene yayin ci gaba da aiki.
Shugaban karamar hukumar, Abdulmumin Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa.
Sanarwar wacce aka fitar ta ofishin mai bai wa shugaban shawara na musamman ta ce hafsoshin sojan ruwan sun kasance biyar kuma suna ci gaba da aiki a lokacin harin.

“An tabbatar da jami’ai biyu sun mutu sannan biyu sun jikkata kuma a yanzu haka suna karbar magani a asibiti. Jami’i guda ya tsallake rijiya da baya. ”

A cewar sanarwar, ‘yan bindigar sun kai wa tawagar sojoji biyar hari ne a daidai lokacin da suke ci gaba da aiki a bakin shingen binciken karamar hukumar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button