Tsaro

‘Yan Bindiga Sun Kashe’ Yan Sanda Biyu A Jigawa

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe‘ yan sanda biyu yayin da dayan ya ji rauni a jiya Juma’ar da ta gabata a kauyen Kalgo da ke karamar Hukumar Garki, Jihar Jigawa, Arewa maso Yammacin Najeriya.

Lamarin ya faru ne Jiya Juma’a jim kadan bayan sakin Zainab Isa Zakari, daliba ‘yar ajin (400 Level) a Jami’ar Sule Lamido, Jihar Jigawa da‘ yan ta’adda suka sace a ranar Litinin a kauyen Bosuwa da ke karamar Hukumar Maigatari a jihar.

Ana zargin ‘yan bindigar mambobin kungiyar ta’addanci ne da suka addabi karamar hukumar.

‘Yan bindiga suka sace Zainab daga gidanta a ranar Litinin da misalin karfe 1 na dare.

Rahotanni sun cewa ‘yan bindigan sun yiwa‘ yan sandan kwanton bauna kuma sun kashe jami’ai biyu yayin artabun da ya biyo baya yayin da na ukun ya samu raunuka.

‘Yan sandan da suka rasa ransu suna aiki ne a hedikwatar’ yan sanda na Maigatari kuma an ce sun yi hanzarin zuwa kiran gaggawa lokacin da ‘yan bindigar suka yi musu kwanton bauna. ‘Yan bindigar sun kai hari ne a kauyen Kalgo.

Dan sandan da ya jikkata na karbar kulawa a babban asibitin Gumel.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa, Abdu Jinjiri, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Jinjiri ya ce har yanzu bai samu cikakken bayanin abin da ya faru ba.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button