Labarai

Yan bindiga sun Sace Dan Majalisa a jihar taraba.

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga da ba a san su ba sun yi garkuwa da wani mamba mai wakiltar mazabar Nguroje a majalisar dokokin Taraba, Barr. Bashir Mohammed.

An sace Mohammed daga gidansa da misalin karfe 1 na dare, ranar Laraba, kamar yadda wata majiya daga danginsa ta shaida wa DAILY POST.

Dan majalisar ya kasance Shugaban Kwamitin Majalisar kan Labarai.

Wannan ya faru ne kusan awanni 24 bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin sakin sojoji kan masu satar mutane.

Buhari ya ce zai tabbatar da sojoji sun kawar da masu satar mutane da ‘yan fashi a duk fadin kasar.
Yayi magana ne yayin ganawarsa da gwamnonin jihohi 36 jiya a Abuja.

”Muna tunani sosai kan batun satar mutane.

“Za mu ba da damar sojoji su tunkari ‘yan fashi da masu satar mutane su kawar da su,” in ji Buhari.

Har yanzu ‘yan sanda ba su tabbatar da sace dan siyasar ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button