Labarai

‘Yan bindiga sun Sace Kawaye da Iyayen Amarya a Karamar Hukumar Sabuwa ta Jihar katsina

Spread the love

Wasu ‘yan ta’adda da ake wa lakabi da ‘yan bindiga sun kai hari tare da yin awon gaba kimanin angwaye mutun 55 wadanda aka ce suna raka wata amarya a kusa da garin Damari a karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.

Mazauna yankin sun tabbatar a ranar Juma’a cewa an kai harin ne a ranar Alhamis da misalin karfe 9 na dare.

Majiyar ta ci gaba da cewa wasu jami’an tsaron yankin guda uku ne suka rasa rayukansu a cikin gaggawar hadin gwiwa da aka yi na ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

“Yawancin wadanda ‘yan ta’addan suka kai hari tare da sace su, wadanda tuni suka arce a cikin wata budaddiyar mota mai suna canter.

Wadanda abin ya shafa tun farko sun haura 70, yawancinsu abokan amaryar ne, inda wasu da dama suka tsere bayan da suka yi tsalle daga cikin motar da ta tashi a lokacin da ‘yan ta’addan suka sace motar,” inji shi.
Karamar hukumar Sabuwa dai ta sha fama da matsalar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda

Shugaban karamar hukumar Dandume, Alhaji Basiru Musa ya tabbatar da haka.

Yayin da wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba na nuni da cewa wasu ‘yan matan da aka yi garkuwa da su sun yi nasarar tserewa, shugaban ya yi alkawarin tantancewa tare da bayar da bayanai.

Ya kara da cewa duk da cewa matan ‘yan garin Dandume ne, ‘yan bindigar sun tare su ne a kan hanyarsu ta daga karamar hukumar Sabuwa da misalin karfe 9 na dare.

Sabuwa da Dandume na daga cikin kananan hukumomin da ‘yan bindiga ke addabar jihar Katsina.

A wani lamari makamancin haka kuma, an tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga daga dajin Siddi, sun kutsa cikin Tashar Nadaya, kusa da kan iyakar Gazari a karamar hukumar Sabuwa.

An ce masu laifin sun kashe wani mahayin babur ne na kasuwanci sannan suka tafi da babur dinsa.

An kuma bayyana cewa sun bude wuta kan wasu mutane hudu tare da kwace babura.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button