Labarai

‘Yan bindiga sun Sace mutun sittin a jihar zamfara.

Spread the love

Wasu ‘yan bindiga sun afkawa kauyen Lingyado da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da maza da yara sama da 50 a yankin. Jaridar DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa yan bindigan sun afkawa kauyen ne da sanyin safiyar Lahadi a kan babura, uku ga kowannensu kuma dukkansu suna rike da bindigogin AK47. Wani ganau wanda ya zanta da sashen Hausa na BBC ranar Litinin da sharadin kada a bayyana sunansa ya ce ’yan bindigar sun dade suna addabar kauyen tsawon shekaru. A cewarsa, duk da yawan hare-haren, kauyen ba shi da jami’an tsaro sama da shekaru uku. Ya ce: “Fiye da shekaru uku yanzu yawancinmu ba za mu iya kwana a gidajenmu ba, muna kwana a daji. Muna kwanciya tare da tsoron Yan fashi a kowane dare.

“Ba mu da wani taimako na tsaro. ‘Yan bindiga sun sace 60 a kauyen Zamfaran sun Kuma raunata’ yan sanda 3 a karshe mazauna garin sun nemi Agajin gaggawa daga Gwamnatin tarayya data jihar su ta zamfara…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button