‘Yan Bindiga sun sace wasu sabbin Dalibai na wata Makaranta a Jihar Katsina.
Kimanin mako daya da ‘Yan bindiga suka kai hari makarantar sakandaren Kimiyya ta Gwamnati, Kankara suka sace dalibai 344.
Wani gungun ‘yan bindigar da ake zargin’ yan fashi ne sun sace daliban makarantar Islamiyya da yawa a garin Mahuta, karamar hukumar Dandume da ke jihar Katsina.
Kamar yadda Jaridar Katsina Post ta rawaito, an sace daliban Islamiyyar ne a kan hanyarsu ta komawa gida bayan sun yi wata muzaharar maulidi a Unguwar Al-Kasim, wani kauye da ke kusa.
Har yanzu ba a san ainihin adadin daliban da aka sace ba, amma tuni kungiyoyin ‘yan banga a cikin al’umma suka fara aikin ceto.
Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, Gambo Isah, ya ce ya na wajen jihar don tantancewa a hukumance kuma ba zai iya cewa komai kan batun ba.
Tushen Labarin: Orient daily news.