Tsaro

‘Yan Bindiga Sun Sace Yaran Tsohon Kwamishia 2 Da Mutane 2 Har Da Jami’in Tsaron Farin Kaya A Zamfara.

Spread the love

Kakakin rundunar ‘yan sanda a Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ce a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Gusau,‘ yan bindigar sun kashe mutum daya tare da jikkata wani.

Ya ce lamarin ya faru ne a gidan tsohon kwamishina na karamar hukumar a garin Gamji da ke karamar hukumar Bakura a jihar da Asubar Yau Talata.

“Da misalin karfe 4:30 na safe, `Yan bindigan dauke da muggan makamai suka mamaye gidan tare da sace yaransa biyu da wasu mutane biyu ciki har da wani jami’in Farin Kaya Na Civil Defence da ke aikin tsaro a gidan.

“An harbe mutum daya yayin da wata mace ta ji rauni a lokacin harin. Inji shi.

Shehu ya ce rundunar ta tura jami’anta domin ganowa da kuma kubutar da wadanda lamarin ya rutsa da su, tare da kama wadanda suka kai harin.

“Rundunar ta kara tabbatar wa da tsohon kwamishina da kuma dukkanin mutanen jihar cewa za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an sako wadanda suka sace tare da dawo da su gida kamar yadda aka yi wa mutanen da aka sace wadanda suka hada da shugabannin gundumar Basasa biyu da Ruwan Gizo a Talata. Kananan hukumomin Mafara da Bakura.

Ya kara da cewa, “Rundunar tana kira ga jama’a da su guji fuskantar wasu ‘yan bindiga yayin wannan aika-aika amma su kai rahoto ga’ yan sanda ko kuma duk wani jami’in tsaro da ke kusa da su don daukar mataki cikin hanzari. Inji Shi.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button