‘Yan Bindiga sun tarwatsa ɗalibai daga ajujuwansu a Zamfara.
‘Yan Bindiga sun tarwatsa ɗalibai daga ajujuwansu a Zamfara
Wasu ɗalibai da ke karatu a wata makarantar sakandire a unguwar Damaga a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara sun tsere daga ajujuwansu ranar Laraba lokacin da ƴan bindiga suka kai hari unguwar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mazauna unguwar sun ce maharan sun iso ne a kan babura sannan suka buɗe wuta nan take.
A ƙalla mutum 13 ne suka mutu a harin sannan an yi awon gaba da shanu da dama.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa Daily Trust cewa maharan sun iso ne da misalin karfe 1 na rana sannan suka fara harbi.
Ya ce ɗaliban na karatu a makarantar ta je-ka-dawo a unguwar kuma suna hango maharan dauke da makamai suka tsere daga ajujuwansu.
Rundunar Ƴan sanda ta jihar ta ce tana gudanar da bincike kan faruwar lamarin.
Zamfara dai na ɗaya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke tsananin fama da matsalar tsaro.