‘Yan bindiga sun yi awon gaba da ‘Ya’yan Shugaban APC sun nemi miliyan 50, kudin fansa.
‘Yan bindiga sun sace ya’yan shugaban jam’iyyar APC da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, Alhaji Gyare Kadauri Sani, kuma sun nemi kudin fansa miliyan 50.
Wadanda aka sace din sune,- Bashar, Abubakar, Haruna, Habibah, Sufyanu, Mubarak da Armiya, ‘yan fashi sun sace su a ranar Juma’ar da ta gabata a kauyen Kadauri.
“Sun kira ni sun ce ni in biya miliyan 50. don sakin yarana su bakwai ko kuma sun yi gargadin cewa za su kashe su idan ba a biya kudin a kan lokaci ba,” in ji shi.
Lokacin da aka tambaye shi ko ya tuntubi hukumomin da abin ya shafa kan batun, ya ce, “Babu bukatar in gan su tunda suna sane da abin da ya faru da ni kuma ba wanda ya CE komai a kai.
“Ko Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Bala Bello Maru, wanda ya fito daga karamar hukuma ta, bai zo gidana ba don tausaya min ko kira ni a waya ba.” Inji Shi.
Ya kuma koka kan cewa shugaban karamar hukumar, Alhaji Salisu Dangulbi, shi ma bai tuntube shi kan lamarin ba.
Gyare ya kara da cewa “Na ji matukar damuwa; Ina jin kamar ni bako ne kuma ban san abin da zan yi a wannan lokacin ba, saboda ba zan iya biyan kudin da wadannan mutane suka nema aguna Ba.
Yace, Ya lura cewa ba zai iya tara kudin da ‘yan fashin suke nema ba ko da kuwa ya sayar da dukkan kadarorinsa, yana mai cewa, “Na yi wa’ yan fashin bayanin hakan ne a wayar, amma sai dai su yi min dariya kawai.”
Gyare ya yi tir da yadda hukumomin da abin ya shafa ke nuna halin ko in kula game da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya.
Ahmed T. Adam Bagas