‘Yan Bindiga Sunyi Ta’asa A Jihar Neja.

Matsalar Tsaro- Yan bindiga Sun Kashe mutun 1 sun Kore Shanu 150 a Jahar Neja.

Ahmed T. Adam Bagas
A daren Juma’ar da ta gabata ne da misalin karfe 9:30 na dare Yan Bindiga Da yawansu Ya kai mutun Talatin dauke da Gaggan Makamai suka Shiga Kauyika 6 a Karamar Hukumar Shiroro ta Jahar Neja.
Kauyukan da Suka shiga sun hada da:- Zhazhayidna, Kpayituko, Iboru, Ndayainkwo, Mbkwo, da Kudodo duk kansu a Karamar hukumar Shiroro.
Yan Bindigar sun kashe mutun 1 Sannan Sun kore Shanu 150 sun tafi dasu.
Yan kin Shiroro dai yanki ne da ya Dade yana Fuskantar Barazanar Yan Bindiga masu garkuwa da Mutane da barayin Shanu.
Ko a Ranar talatan da Tagabata matasan Shiroro sun Gudanar da zanga zangar Lumana kan Matsalar Tsaro a Gidan sarkin Minna dake Babban birnin Jahar ta Neja.
Allah ya kawo mana Mafita.