Tsaro

‘Yan Boko Haram Sun Kai Hari Borno Da Yammacin Yau, Litinin

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Mayakan Boko Haram sun kai wani mummunan hari da yammacin yau Litinin a Garin Magumeri dake jihar Borno.

Harin ya kasance da misalin karfe 4 na yammacin yaune, kamar yanda Vanguard ta ruwaito. Mun samo muku cewa, wasu dake guduwa daga garin sun bada labarin cewa Sojoji sun yi kokarin hana Boko Haram shiga garin amma sun fi karfin sojojin inda suka afka cikin garin.

Lamarin yasa jirgin yaki ya kasa yiwa Boko Haram din ruwan bama-bamai saboda sun saje da jama’ar gari.

Dan majalisa me wakiltar, Magumeri, Gubio da Kaga a majalisar tarayya, Usman Zannah ya tabbatar da faruwar Lamarin. Ya bayyana cewa Boko Haram sun lalata Na’urar sadarwa dake garin dan haka ba’a iya magana ta wayar hannu da mutanen garin inda yayi fatan Allah ya kai musu dauki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button