Tsaro

‘Yan Boko Haram Sun Kashe Sojoji Sun Kuma Sace Mutane A Borno.

Spread the love

An Kashe Sojoji 9 da Yan Sa Kai 2 A Harin kwantan Bauna.

Kamfanin Dillanci Labaran Faransa (AFP) Ya Rawaito Cewa Yan Boko Haram Sun Sace Fararen Hula Dayawa sun Kashe Sojoji 9 Yan Kato dagora 2 A Jahar Borno Jiya Asabar.

Maharan sun Kai Harin kan Motoci Sama da Dari da Sojoji ke musu Rakiya, Lamarin ya farune a Dai dai Garin Komla dake Karamar Hukumar Damboa dake da Nisan Kilomita 55 daga Maiduguri.

Wani Soja daya Shaidawa AFP yace Maharan Sunyi kwantan Bauna ne kan matafiyan Kuma sunyi Amfani da Manyan Makamai Hadda Roka wajen Kai Harin.

Maharan Sun kwashi kayan Abinci sannan Sunyi Garkuwa da Mutane Da dama Suka Shiga Jejin Sambisa. Inji-AFP

Daga Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button