Tsaro

‘Yan Boko Haram Sun Kashe Sojojin 3 Wasu Da Dama Sun Bace A Wani Sabon Hari Da Sukakai A Borno.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Rahotanni daga jihar Borno dake Arewa maso gabasgin Najeriya na cewa sojoji akalla 3 ne suka rasa rayukansu sannan wasu da dama suka ji rauni wasu kuma suka bace a harin kwantan Bauna da Boko Haram ta kai musu.

Harin ya faru a Jiya, Asabar, a Ladari dake yankin Gamboru, kamar yanda Sahara Reporters ta ruwaito. Mun samo muku cewa, An kwashe awanni 4 ana fafatawa tsakanin Sojojin da Boko haram kamin a tsagaita wuta.

Wata majiyar tsaro tace Boko Haram din sun kwashi kayan yaki da dama a lokacin harin.Mun ruwaito muku cewa Boko Haram na tsananta hare-hare akan sojojin Najeriya a ‘yan kwanakinnan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button