`Yan Boko Haram Sun Kashe Sojojin Najeriya Goma, da dama Sun Bata a Borno.
Jaridar Sahara Reforters ta rawaito Cewa, Sojojin Najeriya 10 sun rasa rayukansu wasu da dama kuma suka bace bayan wani hari da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi musu a jihar Borno.
An kai harin ne a kan babbar hanyar Maiduguri-Damboa ranar Asabar da Ta gabata
Sojojin suna dawowa daga sintiri da aikin kwantar da tarzoma kan ‘yan ta’addar a lokacin da aka kai musu harin, in ji wata majiyar tsaro ta shaida wa Yan Jarida a Yau Litinin.
Ya ce adadin wadanda suka mutu na iya tashi saboda sauran gawawwakin za su iya kasancewa cikin daji Inji Shi.
Maharan sunyi kwanto kusa-kusa. ‘Yan ta’addar sun buya a gefen hanya, suka kuma bude wuta a kan ayarin motocin yayin da suke wucewa.
A karshe dai yace muna da sama da sojoji 10 wadanda suka rasa rayukansu a wannan maharan. Har yanzu mutane da yawa sun bata Inji Shi.
Ahmed T. Adam Bagas