
A Yau Laraba ne ‘yan ta’addar Boko Haram suka fitar da wani sabon faifan bidiyo da ke nuna kisan ma’aikatan agaji hudu da wani jami’in tsaro.
Jaridar SaharaReporters Ta Rawaito cewa an sace ma’aikatan agajin ne a ranar 29 ga watan Yuni yayin da suke tafiya tsakanin Maiduguri zuwa Monguno a Jahar Borno.
A cikin bidiyon daya daga cikin masu tayar da kayar baya, wanda ya yi magana da Harshen Hausa, ya ce an kashe ma’aikatan ba da agaji 5 ne saboda aiki tare da “kafirai da kungiyoyinsu”.
Ya ce, “Wannan saƙko ne mai ƙkarfi ga waɗanda kafirai ke amfani da su don maida mutane zuwa kafirci.Ku Lura da kyau wadanda suke aiki ga kungiyoyin kafirai.
“Kun yi aiki dasu don cimma burinsu amma basu damu da ku ba wannan shine dalilin da yasa muka sace ku, basu nuna kulawa a kan Ku Ba. Muna kira gareku da ku tuba ku juyo ga Allah.
Tabbas za mu kama ku cikin hanyoyin da kuke bi. Idan ba ku hanu ba.
Faifan bidiyon ya nuna wasu mutane dauke da bindigogin kirar AK47 guda biyar ga ma’aikatan biyar a durkushe an rufe musu fuska an daura musu Bindigu a kai sannan.
An yi harbi a lokaci guda kuma an kashe ma’aikatan.
Ahmed T. Adam Bagas