Labarai

Yan fansho a jihar katsina sun bukaci Gwamna Dikko Radda da ya kara musu albashin su na wata-wata.

Spread the love

Abdulrahman Ashura, sakataren kungiyar ’yan fansho ta kasa a jihar ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Daura ranar Litinin.

Ya ce kiran ya yi daidai da sashe na 173 (3) da na 210(3) na kundin tsarin mulkin 1999, wanda ya ce za a sake duba kudaden fansho na ma’aikatan da suka yi ritaya duk bayan shekara biyar ko kuma idan aka duba albashin ma’aikata.

An raba kayan tallafin ga kungiyoyin ma’aikata a fadin kananan hukumomin jihar 34, kuma ba a hada da ‘yan fansho. Wani muhimmin korafe-korafe shi ne batun biyan ma’aikatan kananan hukumomi basussukan fensho na watan Mayun 2012 zuwa Afrilu 2014,” inji shi.

Ya ce, a shekarar 2016 an warware basussukan gratuity, yayin da ba a biya bashin kudaden fansho na wata-wata ba. Ya yaba wa Mista Radda bisa kafa kwamitin da zai yi garambawul ga tsarin fansho na jiha da na kananan hukumomi.

Ya kuma yabawa gwamnan bisa shirinsa na samar da hukumar kula da harkokin fansho a jihar domin magance matsalolin da suka shafi fansho.

(NAN)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button