Tsaro
‘Yan Fashi Sun Kashe ‘Yan Sanda Takwas Da Suka Hada Da DPO A Jihar Kogi.
Daga Haidar H Hasheem Kano
Majiyoyi daga Jihar Kogi na cewa, wasu Manyan ‘yan fashi dauke da muggan makamai sun kashe ‘yan sanda guda takwas ciki har da mai mukamin DPO yayin da suka afkawa bankin First Bank da ke garin Isanlu a jihar Kogi.
Gidan radiyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, a yayin wannan hari wata mata ta rasa ranta sakamakon harsashin bindiga da ya same ta a yayin musayar wuta tsakanin ‘yan fashin da jami’an ‘yan sandan a cewar rahotanni.
Kawo yanzu babu cikakken bayani game da lamarin da kuma adadin rayukan da suka salwanta, amma an ce, daga cikin mutanen da barayin suka kashe har da wasu daga cikin ma’aikatan bankin da kwastamominsu.