Labarai

‘Yan Gudun Hijira Suna Shiga Kungiyar Boko Haram~Gwamna Zulum.

Spread the love

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya shaida wa BBC Hausa cewa kungiyar Boko Haram tana ci gaba da daukar mutane domin su taya ta yaki.

“Gaskiya ne kungiyar Boko Haram na ribatar mutane domin su shiga cikinta kuma hakan kuma abin tsaro ne,” in ji gwamnan.

Sai dai Gwamna Zulum ya tabbatar da cewa “idan har jama’ar da ke sansanonin ‘yan gudun hijra a jihar Borno ba su samu abin da suke so ba musamman damar komawa garuruwansu domin noma to fa dole ne su shiga kungiyar Boko Haram.

“Mutane sun gaji da zama a sansanin masu hijra. Ba sa samun abin da suke so. Dole ne su koma garuruwansu domin samun damar yin noma da kiwo kasancewar babu wata gwamnati da za ta iya samar da ciyarwa gare su mai dorewa,” a cewar Gwamna Zulum.

Dangane da garuruwan da jama’arsu suka koma, Farfesa Babagana Umara ya ce sun samu nasarar mayar da mutane garuruwansu kamar Kukawa da Mafa sannan nan ba da jimawa ba “za mu mayar da mutanen Kawuri.”

“Amma muna fatan sojoji za su kara kaimi wajen ganin an mayar da al’ummar Baga da Marte da Malam Fatori da Guzamala”.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button