Labarai

‘Yan Gudun Hijira Suna Zanga Zangar Yunwa A Borno.

Spread the love

Da safiyar yau Litinin ne masu zaman hijira a Garin Banki dake karamar hukumar bama ta jihar borno suka yi zanga zanga da sukace yunwa Na galabaitar dasu, hukumomi sun barsu da Yunwa.

Jihar borno dai Itace jahar da tafi kowacce jiha yawan ‘yan gudun hijira a Kasar nan.

Ko a ranar Juma’ar da ta gabata gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya Ziyarci ‘yan gudun hijira da aka dawo dasu daga kasar nijar a garin Damasak dake Jihar ta Borno.

Ko a jiya Lahadi Gwamnan Zulum, ya Tura ma’aikata da zasu gyara garin Baga a kokarin gwamnan na maida ‘yan Garin Garinsu domin ci gaba da Rayuwarsu a garinsu kamar yadda suka saba a baya.

Idan baku manta ba, Garin Baga Ta kwashe kusan shekaru Goma babu kowa, bayan ‘Yan Boko Haram sun Tarwatsa Mazauna Garin.

Gwamnan ya tura Wata tawaga da zasu Share Garin su Gyara Rijiyoyi, Kasuwanni Masallatai, Da Sauran Guraren Rayuwar Al’umma, Idan masu gyara garin Sun Gama sai Mazauna Garin Su koma.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button