Yan Kwankwasiyya Sunyi Addu’oi Na Musamman Kan Dan Uwansu da Yabata.
Abubakar Idris (Abu Hanifa Dadiyata) Wani Matashi Ne Dan Asalin Jihar Kano, Mazaunin Jihar Kaduna, Wanda Kuma Malami Ne A Jami’ar Dutsin Ma, Ta Jihar Katsina, Kuma Babban Masoyin Tafiyar Siyasar Kwankwasiyya. Ranar 1st Ga Watan Augustan 2019 Ne, Wasu Mutane Da Ba’asan Kosu Waye Ba, Suka Zo Har Gidansa A Jihar Kaduna Suka Sace Shi, Wanda Kawo Yanzu Kimanin Shekara Guda Kenan Ba’a Ga Inda Dadiyata Yake Ba.
Dadiyata Magidancine Mai Mata Daya, Tare ‘Ya’ya Guda Biyu, Mahaifinsa Da Mahaifiyarsa Suna Raye, Yana Da Yan Uwa, Abokan Arziki, Abokan Aiki, Makobta Da Sauransu, Wanda Da Farko Anyi Tsammanin Yana Hannun Jami’an Tsaro, Amma Bayan Tuntubar Hukumomin Tsaro Na Police, DSS, Da Sauransu, Suka Tabbatar Dadiyata Baya Hannnunsu, Kuma Har Yanzu Basu Samu Nasarar Gano Inda Dadiyata Yake Ba.
Ranar Juma’ar Da Ta Gabata 24/07/2020, Wasu Daga Cikin Abokan Dadiyata, Suka Jagoranci Gudanarda Saukar Karatun Alqur’ani Mai Girma, Tare Da Addu’oi Na Musamman, A Masallacin Gidan Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso Dake Birnin Kano, Da Nufin Allah Ya Bayyana Abubakar Cikin Aminci Da Koshin Lafiya, Tare Da Yin Addu’a Akan Halin Da Wannan Kasa Take Ciki, Na Rashin Ingantaccen Tsaro, Kuncin Rayuwa, Da Sauran Abubuwa Marasa Dadi, Akan Allah Ya Maganta.
A Karshe Anyi Kira Ga Jami’an Tsaro Da Sauran Masu Ruwa Da Tsaki A Harkokin Tsaro, Kan Su Kara Kwazo Wajen Tabbatar Da Dadiyata Ya Kubuta Daga Hannun Wadanda Suka Sace Shi, Domin Ya Dawo Cikin Iyalansa, Ya Cigaba Da Rayuwa Kamar Kowa, Bisa ‘Yancin Da Yake Dashi A Matsayinsa Na Dan Kasar Nan.