Siyasa

‘Yan majalisar wakilai da minista sun yi zazzafar muhawara kan zargin cin hanci da rashawa..

Spread the love

Kwamitin majalisar mai kula da harkokin mata da ci gaban al’umma, karkashin jagorancin Kafilat Ogbara, ta gayyaci ministar bisa zargin almundahana a ma’aikatar ta. 

Kwamitin na binciken zargin karkatar da naira biliyan 1.5 da aka ware domin biyan ‘yan kwangila.

Wasu ‘yan kwangilar sun shigar da kara a gaban kwamitin, bisa zargin rashin biyan kudaden kwangilolin da suka aiwatar a ma’aikatar.

Ba da jimawa ba sai sauraron karar ya rikide zuwa ihu, inda ‘yan kwamitin da ministan suka yi ta zarge-zarge.

“Abin da aka kashe na shekarar 2023 daga ofishin akanta-janar, an fitar da shi ne a asusun ma’aikatar harkokin mata. Eh ko a’a?” Ogbara ya tambaya. 

Marie Ebikake, wata mamba a kwamitin, ta zargi ministar da mayar da ma’aikatan ma’aikatar baya.

“Abin farin ciki, na halarci taron da ya gabata kuma daya daga cikin dalilan da ya sa muka yarda da ke shi ne samun gaskiya daga wajenki, kuma a yau kin karkata…,” in ji Ebikake, kafin ministar ta katse ta.

“Ni ban yarda ba. Ba na son wannan zargi. Ni ba baiwa ga kowa bace,” in ji Kennedy-Ohanenye.

“Ya kamata ta janye wannan maganar da ta ce game da ni. Ba adalci bane a nan. Tarko ne amma ba zan yi tsalle a ciki ba. Ba na jin tsoron komai… babu komai !! ”…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button