Labarai

‘Yan Nageriya ba su da dalilin Jin Yunwa domin zamu iya ciyar da kanmu a Nageriya ~Cewar Shugaba Tinubu.

Spread the love

Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Litinin ya shaidawa gwamnonin da su ci gaba da biyan ma’aikata albashin ma’aikata a jihohinsu har zuwa lokacin da za a kammala tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi.

Shugaban ya kuma ce ‘yan Najeriya ba su da dalilin yunwa saboda kasar na da karfin ciyar da al’ummarta kuma har yanzu tana da isassun kayan da za a iya fitarwa zuwa kasashen waje.

Shugaba Tinubu, wanda ya bayyana haka a lokacin da ya kaddamar da shirin samar da abinci da sarrafa kayan gona a jihar Neja, ya jaddada cewa gwamnatinsa ta jajirce wajen tabbatar da wadatar abinci da kuma kare masana’antun cikin gida domin samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button