Labarai

‘Yan Nageriya ku cigaba da tsammani tare da begen samun ingantacciyar Nageriya ~Sakon Kashim Shettima ga ‘yan Nageriya.

Spread the love

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya yabawa ‘yan Najeriya mazauna kasar Rasha bisa kishin kasa da suke nuna musu, ya kuma bukace su da su ci gaba da kasancewa da fatan samun ingantacciyar Najeriya.

Shettima ya yi wannan yabon ne a lokacin da ‘yan Najeriya mazauna kasar Rasha suka gana da shi a gefen taron tattalin arziki da jin kai na Rasha da Afirka karo na biyu.

Ya ce gwamnatin tarayya ta dukufa wajen ganin an samu zaman lafiya a Najeriya, ya kuma bukace su da su kasance jakadun kasarsu na nagari a koda yaushe.

Tun da farko, Farfesa Maurice Okoli, shugaban kungiyar ‘yan Nijeriya mazauna kasar Rasha, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi la’akari da irin damar da dandalin hadin gwiwar Rasha da Afirka ke bayarwa domin bunkasa tattalin arzikin kasar.

An gudanar da taron koli na tattalin arziki da jin kai na Rasha da Afirka karo na biyu a birnin St. Petersburg na kasar Rasha a ranakun Alhamis da Juma’a.

Yayin da yake taya mataimakin shugaban kasar murnar sakamakon zaben, Okoli ya ce zai yi amfani da ofishinsa wajen cim ma samun abubuwa masu kyau ga Nageriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button