‘Yan Nageriya ku godema Allah da yanzu bama-bamai Basu tashi a kullum ~Buhari
Fadar Shugaban kasa ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi godiya cewa hare-haren bama-baman da suke faruwa a lot Wacce rana a Shekarun baya yanzu sun daina
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya fadi haka a shirin ‘Siyasar Lahadi na Channels Television a ranar Lahadi.
Adesina, wanda shi ne babban hadimin Shugaban kasa kan harkokin yada labarai, yana mayar da martani ne ga korafin da ‘yan Najeriya suka yi game da karuwar rashin tsaro a kasar.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya yi ikirarin cewa anyi wani lokaci a kasar da bama-bamai shida za su tashi a rana guda amma tun lokacin da mai gidansa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya zama Shugaban kasa, kashe-kashe ya ragu.
Ya ci gaba da da’awar cewa kashe-kashe da tashin bama-bamai a yanzu ba su cika faruwa ba kasancewar yanzu kasar ta yi makonni da watanni ba tare da wani tashin hankali ba.
Adesina ya fadi haka ne yayin da yake mayar da martani game da kashe-kashe biyar da suka faru a kwanaki ukun da suka gabata.
Lokacin da aka tambaye shi ko tsaro ya inganta, sai ya ce, “Ee, akanyi mako, makonni biyu ko da a wata cewa ba kuji abubuwan tashin hankali suna faruwa ba sabani a can baya da suke faruwa a kullum.
Ka yi magana game da tashin bam ɗaya a cikin kwana uku ko huɗu. Akwai wani lokaci a wannan kasar da bama-bamai suke tashi kamar wuta a kowace rana. Za a iya samun tashin bama-bamai guda biyar, shida a rana guda. Yanzu, zaku iya samun watanni biyu, uku ba tare da wani batun tashin bam ba.yakamata mu zama masu godiya don domin samun rahama. Duk wata jinƙai da muka samu, to mu yi godiya a kanta, kuma kada mu tsaya a kan abubuwa marasa kyau su kaɗai.
“Rayuwa tana daukar wahala da sassauci tare. Don haka, wani lokacin mukan ga lokacin da abubuwa suka ci gaba na tsawon kwanaki, tsawon makonni ba tare da wani mummunan ci gaba ba, bari mu jaddada wadancan… Muna da kalubale amma wadannan ba su ne masu dorewa a kasar ba.
Lokacin da aka tambaye shi ko Buhari ya iya kawar da Boko Haram kamar yadda ya yi alkawari lokacin kamfen dinsa, Adesina ya ce dole ne a bayyana cewa Shugaban ya yi wasu alkawura ne a matsayin dan adawa ba jami’in gwamnati ba.
Ya yi ikirarin cewa an ci karfin ‘yan ta’addan ta hanyar fasaha amma har yanzu suna aiki a wasu yankuna a wani karamin mizani.
Adesina ya lura cewa Shugaban kasar ya fada a makon da ya gabata cewa hukumomin tsaro na iya yin mafi kyau wanda ke nufin akwai wani abu da yake son gani.
Mai taimaka wa shugaban kasar ta kuma yi tir da ikirarin da tsohuwar Ministar Ilimi, Oby Ezekwesili ta yi, cewa sacewa da ceto fiye da ’yan matan makarantar Kankara 300 da alama abin shakku ne.
Ya ce amincin gwamnatin Buhari tana nan daram.