Lafiya

‘Yan Najeriya miliyan 54 da sauran ‘yan Afirka za su yi zama kurame nan da shekarar 2030: WHO

Spread the love

Rahoton ya bayyana abubuwa da yawa da ke haifar da yawaitar asarar ji a yankin Afirka.

Kimanin mutane miliyan 40 ne ke fama da matsalar ji a yankin Afirka, amma adadin zai iya haura miliyan 54 nan da shekarar 2030 idan ba a dauki matakan gaggawa na magance matsalar ba, a cewar wani sabon rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

Rashin ji yana da matukar tasiri ga rayuwar bil’adama da tattalin arzikin bil’adama, inda ake kashe dalar Amurka biliyan 27 a duk shekara, a cewar rahoton yanayin kula da kunne da ji a yankin Afirka na WHO, wanda aka kaddamar yau yayin taron kolin Afirka kan nakasar ji a birnin Nairobi na kasar Kenya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button