‘Yan Najeriya Na Rokeku Da Ku Yi Hakuri Kuci Gaba da Zama A Gida~Shugaban Kasa Muhammadu Buhari…….
Sanarwar da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar, ta jaddada cewa, gwamnatin tarayya za ta bullo da shirin tallafa wa ‘yan Najeriya don rage musu radadin zaman gida na dole a daidai wannan lokaci, musamman ma a jihohin Lagos da Ogun da kuma Abuja, inda aka sanya dokar hana fita.
Shugaba Buhari ya mika godiya ga daukacin al’ummar kasarnan bisa hakurinsu da kuma yadda suka bada goyon bayan kawo karshen wannan cuta.
“Mun fahimci cewa, akwai ‘ya’yan da suka gaza ziyartar iyayensu da kuma tsofaffin da aka kebe su daga matasa. Kazalika akwai wadanda ke rayuwa hannu-baka-hannu kwarya da ke shan walaha a wannan lokaci.” inji shugaban.
A ranar 29 ga watan Maris da ya gabata ne, Buhari ya shelanta dakatar da zirga-zirga a Lagos da Abuja da Ogun har tsawon kwanaki 14, a wani mataki na hana yaduwar coornavirus.
Ahmed T. Adam Bagas