‘Yan Najeriya sun amince da majalisar dokokin Najerya – Shugan majalissar Dattijai.
Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce Majalisar Dokoki ta kasa tana da kwarin gwiwar ‘yan Nijeriya.
Ya kawo misali da yawan koke-koke da aka gabatar a gaban Majalisar ta tara.
Lawan yayi magana ne a ranar Talata yayin fara taron.
Ya ce katsalandan din majalisun tarayyar na zama cikin sauri ga begen talakan Najeriya a kokarin neman Adalci.
Lawan ya yabawa kwamitin da Sanata Ayo Akinyelure ke jagoranta kan da’a, gata da kuma koke-koken jama’a game da matakan da suka dace kan al’amuran da majalisar ta gabatar musu.
“Majalisar kasa na da kwarin gwiwar yan Najeriya. Aikin bai-daya na shari’a baya ga wakilci, dokoki, kuma ba shakka, sanya ido.
“Ina so in taya kwamitinmu na da’a, gata da kuma koke-koken jama’a don yin aiki tukuru da kuma samun sakamako.
Shugaban majalisar dattijan ya kara da cewa “Muna karbar koke-koke a nan saboda mun iya magance matsaloli masu yawa”.