Siyasa
‘Yan Najeriya suna kokarin bin dokarka ta saka takunkumin rufe baki da hanci amma kai kuma kana karya dokar, Jam’iyar adawa ta PDP ta caccaki Shugaba Buhari.
Jam’iyyar PDP ta caccaki shugaban kasa, Muhammadu Buhari saboda zuwa wajan sabujta rijistarsa ta APC a mahaifarsa Daura ba tare da saka takunkumin rufe baki da hanci ba.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya je Daura inda inda yake hutun kwanaki 4 dan yin wannan rijista kuma an ganshi a wajan rijiatar ba tare da saka takunkumin ba.
Kakakin PDP, Kola Ologbondiyan ya bayyana cewa wannan abin takaici ne yanda Shugaba Buhari ya saka dokar saka takunkumin rufe baki da hanci da kuma bada Tazara amma shi baya bin wannan doka.
Saidai a martanin bangaren shugaban kasar yace, ai idan mutum zai yi magana da manema labarai dole zai cire takunkumin dan haka PDP surutune kawai take na jam’iyyar da ta kama hanyar Lalacewa.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe