Rahotanni
‘Yan Sanda Sun Harbe Masu Zanga Zangar #EndSars 5 a Abuja.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta Rawaito cewa “‘Yan Sanda Sun Harbe mutane 5, cikin masu Zanga Zangar #EndSars a Birnin Tarayya a Yau Talata.
Masu zanga Zangar dai Sun Dauki Tsawon kwanaki Sunayi a Tankin Kudancin Kasar Nan, da Birnin Tarayya.
Ko a Jiya litinin ma wasu ‘yan Daba Sun Farwa Inda Masu zanga zangar ke ajiye Motocinsu, Inda Suka kone Motoci sama da 100, Na Masu Zanga zangar a Abuja.
Ko a Legas Sai da Aka sanya Dokar Hana fita a Jihar na Tsawon Awanni 24 domin Yanayin da zanga zangar ta Chanja a Can.
Ahmed T. Adam Bagas