Tsaro

‘Yan Sanda Sun Kasa Kuɓutar Damu, Sai Da Muka Biya Miliyan N5m Zuwa Miliyan N6m Kowannenmu Kafin Mu Kuɓuta Daga Hannu Masu Garkuwa – Inji Jami’an Road Safety Wadanda Akai Garkuwa Dasu.

Spread the love

Wasu daga cikin jami’ai ashirin da shida da aka sace kwanan nan a yankin Maraba-Udege na karamar hukumar Nasarawa da ke jihar Nasarawa sun bayyana cewa kafin su samu’ yanci daga hannun wadanda suka sace su sun biya kudin fansa na N6 zuwa N5 million kowannensu.

Wadanda lamarin ya rutsa da su, sun bayyana yadda suka suka kubuta ga wa sashen Hausa na BBC, sun ce ’yan uwansu uku ne suka kawo kudin suka mika su ga masu garkuwar sannan suka kubuta.

Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, wadanda ba sa son a buga sunan su sun shaida wa jaridar Daily Independent cewa lokacin da ‘yan uwansu suka zo don kwato musu ‘yanci sun nemi masu garkuwar su koma garin Nasarawa da kudin a saka musu a daya daga cikin bankunansu amma sukaki.

Ya ce: “’ Sun sako mu ne bayan ‘yan uwanmu sun biya Naira 6 zuwa miliyan 5 kowannensu kafin a sake mu.

Ina kallon ‘yan uwanmu yayin da nake suke mika kudin ga masu garkuwar.”

“A ranar da danginmu suka zo don a sako mu, sun dauke mu a wannan rana har sai da aka biya su kudin.

Sun umurce mu cewa direba ne kawai zai zo ya biya kudin, ”in ji shi.

“Sun koma karamar hukumar Nasarawa tare da direban don neman kudin. Kuma lokacin da direban ya kawo kudin sai aka nemi su tsaya a gefe.”

A cewarsa, bayan direban ya biya masu garkuwar sai suka koma daji suka fara harbi a iska lokaci-lokaci don yi masu barazana.

Sun ce Kowanne danginsu sun biya Naira miliyan 6 a matsayin kudin fansa kafin a sake su.

Sun kara da cewa kudin da wasu daga cikin su suka biya sun kai Naira miliyan 5, suna mai tabbatar da cewa babu wani daga cikin ‘yan sanda da ya kubutar da su.

Gwamnati ba ta san yadda danginsu suka samu kudi ba, kuma a shirye suke da a taimaka musu, suna mai cewa da ba su biya kudin fansa ba da masu garkuwar sun kawar da su.

Dangane da zargin da wadanda abin ya shafa suka gabatar wa ‘yan sanda, kwamishinan‘ yan sanda a jihar Nasarawa, Mista Bola Longe, ya karyata zargin.

A cewarsa, “Ban san ko an biya wani fansa ba.” Kalaman nasa: “Masu satar mutane makiyanmu ne kuma ba za mu iya shiga wata tattaunawa ta neman fansa tare da abokan gaba ba.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button