Labarai
‘Yan Sanda Sun Kashe Mambobin IPOB 2 a Enugu.
Haramtacciyar Kungiyar nan Mai fafutukar Ballewa daga Najeriya ta kafa Kasar Biafra ta hadu da Fushin Mahukunta yau a Enugu.
A artabun tsakanin mambobin IPOB da Jami’an Tsaron DSS ya Yi sanadiyar Mutuwar Mambobin IPOB 2.
Sai dai Wani ganau ya Shaidawa Jaridar The Natio cewa Jami’an Tsaron Sun kama ‘Yan IPOB Sama da guda 10 sun tafi dasu.
Jaridar Punch Tace tayi kokarin jin Ta bakin Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Ahmad Abdurrahman amma Abin ya Ci tura.
Wannan na zuwane dai dai lokacin da Tsagerun Yankin Niger Delta ke Ikirarin Zasu Fara Cigaba da Fasa Bututun Mai Tunda Gwamnatin Tarayya ta Daina Basu Kudin da ta saba Basu.
Ahmed T. Adam Bagas