‘Yan Sanda sun koma rike jakar matan manya Maimakon yaki da ta’addanci~ El’rufa’i
Gwamna El-Rufa’i ya bayyana cewa yawan ‘yan sanda a Najeriya basu isa ba, sannan kuma ya yi zargin cewa wasu daga cikinsu na yin ayyukan da ba na’ yan sanda ba kamar daukar jakar hannu ta matan manyan mutane.
A cikin hirarsa da gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin, 30 ga Nuwamba, Gwamnan ya dage cewa rarraba aikin ‘yan sanda ita ce hanyar da za ta bi da Najeriya.
Ya ce;
“A koyaushe muna Cewa dunkule jimillar ‘yan sanda waje ɗaya a tarayya ba ya aiki; Najeriya ita ce kasa daya tilo a duniya da ke da tarayyar ‘yan sanda jimillar daya tilo.
“Mun gabatar da hujjar cewa ya kamata a bar jihohi su mallaki nasu‘ yan sanda kuma hatta kananan hukumomi ma a ba su damar yin aikin ’yan sanda
“Yawan‘ yan sanda da muke da su a Najeriya bai isa ba, bai kai rabin abin da muke bukata ba kuma kaso mai yawa daga cikinsu suna gudanar da ayyukan da ba ‘yan sanda ba kamar daukar jakunkuna na matan manyan mutane.
“Muna bukatar samun sahun‘ yan sanda mafi girma a Najeriya kuma hanya daya tilo da za a cimma hakan cikin hanzari shi ne a gyara Kundin Tsarin Mulki tare da sanya ‘yan sanda a cikin jeri kamar yadda Kwamitin Tarayya na Tarayya ya ba da shawarar mu samu‘ yan sanda da yawa. . ”