Tsaro

‘Yan Sanda Sun Kubutar Da Sojoji Daga hannun ‘Yan Boko Haram….

Spread the love

Bayan Kai hari A Borno ‘Yan ta’addar sun kashe wasu jami’an tsaro tare da kame wasu yayin harin da aka kaiwa sojoji masu sintiri.

Rundunar ‘yan sanda ta Najeriya da ke yaki da ta’addanci ta ce ta kubutar da wasu sojoji biyu da mayakan Boko Haram suka sace a baya.

PRNigeria ta rawaito cewa ‘yan ta’addar sun kashe wasu jami’an tsaro tare da kame wasu bayan wani hari da aka kaiwa sojoji kan sintiri.

Wannan ya zo ne bayan sojojin Najeriya sun murkushe wani yunƙuri da ‘yan ta’adda suka yi na kame shingen sojoji a cikin garin Maiduguri ranar Litinin.

Dangane da rahoton da PRNigeria ta ruwaito, an sanar da cewa “A ranar 14.30 na Yuli 13, Yuli2020, ‘yan Boko Haram sun yi awanin a hanya sun yi kwanton bauna a kan hanyar Auno tare da kashe sojoji biyu da sace wasu da kuma kwace biyu daga cikin motar sojojin.

“Yan bindigar suna dauke da indigogin AK 47 da ba a bayyana adadinsu ba.

Sashin Yaki da Ta’addanci na Yan Sandan Najeriya a kan matakin (aiki), a yankin ya biyo bayan ‘yan ta’addan.

Bayan artabu da ‘yan bindigar sun sake kama wata babbar bindiga da kuma kubutar da sojoji biyu da ransu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button