Labarai

‘Yan Sanda Sun Yi Nasarar Shawo Kan Saurayin Da Ya Dauka Alwashin kashe Kansa Idan Bai Auri Hanan Buhari.

Spread the love

‘Yan sanda sun shawo kan saurayin da ya dauka alwashin kashe kansa idan bai aura Hanan Buhari

Wani matashi Abba Ahmad ya hakura da shirin da ya yi na kashe kansa sakamakon rashin samun damar auren diyar Shugaba Muhammadu Buhari, Hanan Buhari.

Ahmad ya hakura ne bayan shawarwari da jami’an rundunar yan sandan Najeriya suka bashi kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Ahmad, dalibin jami’ar Maitama Sule ta Kano (tsohuwar jami’ar North West) ya dade yana aika sakon neman Hanan ta aure shi a Facebook da Instagram.

Matashin da mahaifinsa ya rasu tun a shekarar 2013 ya shaidawa jama’a cewa kyawun Hanan da karatun da ta yi ne ya ke burge shi.

Hanan, mai shekaru 22 ta yi karatu ne a fanin koyon daukan hoto a Jami’ar Ravensbourne da ke Ingila.

Ina kaunar Hanan ne saboda kyawun fuskarta, karatun boko da ta yi da kuma gaskiya irin na mahaifinta (Shugaba Buhari).

“Na yi kokarin sanar da ita amma ban san ko sakon ya isa wurin ta ba,” in ji Ahmad.

Ya rubuta a shafinsa cewa zai kashe kansa idan Hanan ta auri wani namiji daban a ranar Juma’a.

A lokacin da Aka tambayi dalilin da yasa zai kashe kansa saboda mace, ya ce: “Na fada ne kawai

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button