Tsaro

‘Yan Sanda Sunyi Gagarumar Nasara Akan ‘Yan Ta’adda A Katsina.

Spread the love

Jami’an tsaro a Katsina sun kashe ‘yan fashi 15, tare da kama 50 a jihar ta Katsina, kamar dai yadda kwamishinan ‘yan sandar jihar Sunusi Buba ya shaidar da hakan.

Ya kuma kara da cewa sun samu nasarar karbe bindigu kirar AK 47 guda 9, da wasu bindugu na daban guda 20, da mashina 20, da motoci biyu, da sauran su.

Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin da ‘yan ta’adda suke cin karensu babu babbaka, ‘yan fashi barayin shanu da kuma masu garkuwa da mutane.

Daga Bappah Haruna Bajoga

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button