Kasashen Ketare

‘Yan sandan Ƙasar Saliyo sun cafke wasu manyan jami’an Sojoji bisa yunkurin zagon kasa ga dimokradiyya

Spread the love

Wadanda ake zargin dai sun yi niyyar haifar da tarzoma ne a fadin kasar bisa dalilin zanga-zangar da za a yi, kamar yadda bayanan da ‘yan sanda suka gano.

Hukumomin kasar Saliyo sun kama wasu manyan jami’an soji bayan samun sahihin bayanan sirri da ke nuna cewa suna aiki don dakile dimokuradiyyar kasar da kuma yunkurin tayar da tarzoma a kan ‘yan kasar.

“Game da haka, an kama mutane da yawa kuma wadanda ake zargin suna taimaka wa ‘yan sanda wajen bincike,” in ji wata sanarwa daga hedkwatar ‘yan sanda a Freetown, Saliyo, da ke kan titin George.

‘Yan sanda sun yi kamen ne domin hana hambarar da gwamnatin shugaba Julius Maada Bio ta dimokuradiyya, kamar yadda ya faru a makon da ya gabata a jamhuriyar Nijar a lokacin da sojoji suka hambarar da shugaba Mohamed Bazoum.

Wadanda ake zargin dai sun yi niyyar haifar da tarzoma ne a fadin kasar bisa dalilin zanga-zangar da za a yi, kamar yadda bayanan da ‘yan sanda suka gano.

“Bincike na farko ya nuna cewa wadannan mutane sun shirya yin amfani da zanga-zangar lumana tsakanin 7 ga watan Agusta zuwa 10 ga Agusta, 2023, a matsayin hanyar kai munanan hare-hare kan cibiyoyin gwamnati da ‘yan kasa masu zaman lafiya,” in ji sanarwar.

“Duk da ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya da ribar dimokuradiyya, akwai daidaikun mutane a cikin gida da waje da ke ci gaba da aiwatar da ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar,” in ji ‘yan sandan Saliyo, amma sun tabbatar da cewa bangaren tsaro na kasar ya san halin da ake ciki.

Dangantaka tsakanin kasashe mambobin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta samu rarrabuwar kawuna bayan kasashen Burkina Faso da Mali sun kulla kawance da jamhuriyar Nijar, inda suka koma kasar Rasha domin neman taimako wajen samar da makamai domin dakile hare-hare daga shiga tsakani na sojin dake shirin kwato Nijar daga mulkin soja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button