Siyasa

Yan Siyasa Suna Amfani Da Rashin Tsaro Don Wata Manufa Ta Su, Inji Gwamna Matawalle.

Spread the love

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce ‘yan siyasa suna da alhakin matsalolin rashin tsaro da ke addabar kasar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da ya yi jawabi a sansanin sojoji na musamman a garin Faskari.

Matawalle ya ce, “mu, ‘yan siyasa, za a zarge mu saboda matsalolin tsaro da ke addabar al’ummominmu. Ya tabbata cewa wasu yan siyasa suna amfani da rashin tsaro don cimma burin su na siyasa.

“Za su yi rige-rigen zuwa kafofin watsa labarai don bayar da rahoton kai hare-hare daga wasu ‘yan fashi ko kuma wasu ta’addanci.

“Ga wadannan ‘yan siyasan, siyasa ba batun sadaukar da kai ne ga kyautata rayuwar mutane ba, agurin su siyasa don mulki ne kawai ba don komai ba.

Amma, ya tabbatar da cewa tsaro da tabbatar da tsaro ba kawai alhakin Shugaban kasa, Manjo-Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ko Gwamnoni, ko shugabannin ma’aikata bane, amma na kowane dan kasa mai kishin kasa ne.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button