Labarai

‘Yan ta’adda sun Addabi Al’ummar garin Magamin jihar Zamfara suna neman Daukin jami’an Tsaro

Spread the love

Al’ummar Garin Magami dake yankin ‘Karamar hukumar Gusau, sun koka kan yadda ‘Yan ta’adda suka Addabi yankin .

Al’ummar yankin Gundumar magami, suna cikin tashin hankali da fargaba bisa Yadda suke fuskantar barazanar daga ‘yan ta’adda, Akwai ‘kauyikan da Koh bacci basayi saboda zullumin kawo musu Hari daga wanan ‘yan ta’addar

Wani mazaunin Yankin na Magami, yasheda Mana Yadda ‘Yan ta’adda A wanan Yankin suke sawa wadanan ‘Kauyika Doka hatta Gonaki basa iya fita don suyi noma ya ‘kara da cewa Gonaki jama’a sun Isa girbi A ‘Kauyikan nasu Amma saboda tsoron ‘Yan ta’adda, suna kasa zuwa Su Girbe Abunsu Wanda hakan ba ‘Karamar barazana bace gares

 "Ya 'kara Dacewa da zarar kaje gonarka zasuyi Garkuwa dakai sunemi 'Kudin fansa sai Anbiya 'Kudi masu yawa kafin su saki mutum "A cewar  Salisu hasheem ,wani mazaunin Yankin Garin magami.

Akwai bukatar Gwamnati da jami’an tsaro da sukaiwa wadanan Al’ummar dauki domin samun damar gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar Hankali. daga Abdulrashid Abdullahi,Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button