Labarai

‘Yan ta’adda sun kashe mutu 5 Yara masu Shekaru daya Daya.

Spread the love

An kai hari kan wasu fulani makiyaya dake Kauru a karamar hukumar Lere dake jihar Kaduna inda aka kashe yara masu shekaru tsakanin 1 zuwa 5.

Kwamishinan harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya bayyana cewa fusatattun matasane suka kai harin na ramuwar gayya bayan harin da aka kai a Gora Gan, Karamar hukumar Zangon Kataf da ya kashe mutane 7 ranar Alhamis.

Yace harin farko an kaishine a Unguwan Idi dake Kashuku a karamar hukumar Kauru inda akashe Mustapha Haruna me shekara 1, sai Ya’u Kada me shekara 1, Saidu Abdullahi, shima me shekara 1, Zainab Zakari, itama me shekara 1, Sadiya Abdullahi me shekaru 5, sai A’isha Abdullahi me shekara 1. Da kuma wata mata da aka kona kurmus.
Yace mutane 5 sun bace, ba’a san inda suke ba amma jami’an tsaro na nemansu sannan kuma an kone bukkoki 6. Yace akwai kuma mata 2, A’isha Muhammad da Sadiya Abdullahi wanda suka jikkata a harin an kaisu Asibiti suna samun kulawa.

Yace a kauyen Ningi dake karamar Hukukar Lere ma an jikkata wasu Fulani 2 inda suma an garzaya dasu Asibiti.

Yace gwamnan jihar Kaduna,  Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yayi Allah wadai da harin sannan ya aikewa iyalan mamatan gaisuwa da kuma fatan wanda suka jikkata, Allah ya basu Lafiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button