‘Yan ta’adda sun kashe mutun 348 sun Kuma sace 411 duk Acikin wata daya a Wasu jihohin Nageriya.
Akalla mutane 348 suka rasa rayukansu sakamakon munanan hare-hare a fadin Nijeriya a watan Disambar na bara; yayin da aka sace Mutun 411, wani rahoto da wata kungiya mai zaman kanta, Nigeria Mourns ta fitar.
Rahotan wanda aka buga a ranar Litinin, ya nuna cewa mutane 315 cikin 348 da aka kashe fararen hula ne; yayin da wasu 33 suka kasance jami’an tsaro.
An tattara bayanan ne, a cewar rahoton, ta hanyar amfani da rahotannin jaridu da kuma iyalai don bin diddigin kashe-kashen mutane.
Jihar Borno, wacce ke fama da rikice-rikicen kungiyar Boko Haram da mambobin kungiyar ISWAP, daga cikin jihohi 27 da abin ya shafa, ita ce ta fi samun alkaluma masu matukar tayar da hankali a cikin wannan watan inda mutane 70 suka mutu.
Alkaluman wadanda suka mutu a kowacce daga cikin jihohi 27, a cewar rahoton, su ne: Borno, 70; Kaduna, 64; Nijar, 26; Katsina, 24; Ogun, 23; Zamfara, 19; Benue, 17; Edo, 17 ’Delta, 14; Ebonyi, 13; Adamawa, 8; Oyo, 6; Ondo, 6; Bayelsa, 5; Babban birnin tarayya, 5; Legas, 5; Koguna, 4; Filato, 3; Imo, 3; Kuros Riba, 3; Kogi, 3; Jigawa, 3; Taraba, 2; Anambra, 2; Kano. 1; Osun, 1 da Enugu, 1.
Rahoton ya nuna mutane 136 da wasu da ake zargin ‘yan fashi ne suka kashe, mutane 66 da wasu mutane da ake zargin’ yan kungiyar Boko Haram ne ko kuma reshensu na ballewa Zuwa ISWAP suka kashe; kuma 60 ta cikin rikice-rikicen kungiyoyin asiri.
Bugu da kari, rikice-rikicen kabilanci, a cewar rahoton, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 41; yayin da mutane 30 suka mutu a wasu keɓewar kai hare-hare, takwas da makiyaya suka kashe da kuma mutane bakwai ta hanyar kisan gilla.