Rahotanni

‘Yan ta’adda sun kashe mutun bakwai 7 a Zangon kataf ta kaduna.

Wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne, sun kashe mutane bakwai a daren Alhamis a Gora Gan, karamar hukumar Zangon-Kataf da ke jihar Kaduna.

Ku iya tunawa cewa a farkon wannan shekarar, wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne sun mamaye kauye guda lamarin da ya haifar da asarar rayuka da lalata gidaje da sauran abubuwa masu daraja.

Harin na ranar Alhamis, a cewar wata majiya mai tushe, biyar daga cikin mutane bakwai din da ake zargin Fulani makiyaya sun kashe ‘yan gida daya ne.

Wani mazaunin ya sanar damu cewa wata tsohuwa ta ji rauni sosai kuma tuni aka garzaya da ita asibiti don yi mata magani.

Ya kara da cewa, “A yanzu haka da nake magana da ku, za mu zagaya yau da safiyar yau don sanin ainihin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata.

Hakanan gidaje da yawa maharan sun lalata kawo yanzu ba’a tabbatar da yawan gidajen da aka lalata ba.

Majiyar ta bayyana cewa maharan sun zo da yawa kuma sun afkawa kauyen da misalin karfe 8 na dare.

“Muna farin ciki cewa jami’an tsaro sun zo daren jiya don ceton lamarin kuma kamar yadda nake magana da ku, har yanzu suna nan don tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi,” in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button