‘Yan Ta’adda Sun Kashe wani Jigo a Jam’iyyar PDP sun sace ‘Yan Mata 3 a Neja.
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jigon jam’iyyar (PDP) a gundumar Kampala da ke ƙaramar hukumar Bosso a jihar Neja.
Mamacin Alhaji Ahmodu Mohammed, ya gamu da ajalinsa a hannun ‘yan Bindigar ne bayan sun kawo masa hari.
‘Yan bindigar sun taba kai wa marigayin hari a baya, amma ba suyi nasarar kashe shi Ba sai a wannan Lokacin.
Wani ganau ya ce ‘yan fashin, waɗanda yawansu ya kai 15, suna ɗauke ne da makamai irin su adda da sauransu.
“An harbe shi sau da yawa kafin daga bisani ya mutu,” in ji shaidar gani da ido.
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Neja, Alhaji Tanko Beji, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya kuma tabbatar da sace ‘yan matan 3. Ya ce abin takaici ne matuƙa cewa an ɗauki ‘yan matan 3 kamar yadda ya ce bai san ko za a taɓa samun kubutar dasu a kan lokaci ba.
Ya kuma ce an yi jana’izar mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, rundunar ‘yan sandan jihar Neja ba ta mayar da martani kan wannan lamarin ba.
DagaAhm ed T. Adam Bagas