Labarai

‘Yan ta’adda sun kashe wasu mutane takwas a Karamar Hukumar jibia dake jihar Katsina.

Spread the love

A yayin harin da aka kai a daren Lahadi, an ce mutane hudu a cewar shaidun gani da ido, sun samu raunuka, yayin da wasu biyu suka bace

Akalla mutane takwas ne suka mutu bayan wasu da ake zargin ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai sun kai hari a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.

A cewar gidan talabijin na Channels, wani mazaunin garin a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Litinin din da ta gabata, ya ce ‘yan ta’addan da yawansu sun kai harin ne a kan hanyarsu ta dawowa daga kauyen Kukar Babangida zuwa unguwar Yan Gayya.

Ya bayyana cewa wadanda aka kashe tsakanin shekaru 22 zuwa 47 dukkansu ‘yan kauyen Yan Gayya ne kuma an yi jana’izarsa a safiyar ranar Litinin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Wa yanda suka rasa ransu “Su ne Malam Sani Na Gogara Mai shekaru 47; Yusuf Dan Karaminsu, Mai shekaru 22; Yusuf Jari mai shekara 50, Sale Lami mai shekara 45; Dan Hameme Mai shekaru 45; Malam Shafa’i Mai shekara 35; Malam Dikke mai shekara 45 da Bishir Sani mai shekara 30.

“Kuma wadanda suka samu raunuka sun hada da Bilyaminu Yan Gayya, Malam Jafaru, Alhaji Lawal Dadi da Dan Husama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button