Tsaro

‘Yan Ta’addan Boko Haram Sun Kashe Sarakunan Gargajiya 13, Da Masu Unguwanni Da Dama A Borno~Shehun Borno.

Spread the love

Alhaji Garbai Elkanemi, Shehun Borno, ya ce an kashe hakimai 13 da masu unguwanni da yawa (Bulamas) a masarautarsa ​​lokacin da ake fama da rikicin Boko Haram.

Sarkin ya bayyana hakan ne a garin Maiduguri yayin ziyarar girmamawa da tawagar kwamitin majalisar dattijai kan Ayyuka na Musamman karkashin jagorancin Sanata Abubakar Yusuf suka kai masa.

Sanatocin sun je jihar Borno ne domin tantance ayyukan hukumar bunkasa yankin arewa maso gabas.

Basaraken ya yi ikirarin cewa rikicin Boko Haram ya fara ne a jihar a watan Yulin 2009 bayan wani rashin jituwa tsakanin kungiyar Izala da Yusufiya.

Ya ce, “A hankali, sai suka kwashe ayyukansu daga Maiduguri zuwa hedkwatar karamar hukumar da sauran garuruwan da ke cikin jihar. “A yayin gudanar da ta’addancinsu, majalisar masarautar ta rasa kimanin hakimai 13 baya ga masu Unguwanni da yawa, wadanda aka kashe a yankunansu.

Ayyukan ‘yan ta’addan ba su hana gundumominmu da shugabanninmu na kauyuka yin kwazo ba wajen kai rahoto ga jami’an tsaro. “

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button