Yanke Hukuncin Kisa Saboda Batanci Take Hakkin Dan Adam Ne, Inji Wata Musulma Me Rajin Kare Hakkin Mata.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
A jiyane dai muka ji cewa wata kotun shari’ar Musulunci dake Hausawa, Kano ta yankewa matashi Yahaya Aminu Sharifai hukuncin kisa saboda samunshi da laifin batanci ga Fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).
Wannan hukunci ya samu karbuwa wajan Musulmai daga Arewa inda wasu kuma daga kudu suka rika sukarsa.
Wata me kare hakkin mata, Fakhrriyya Hashim ta yi Allah wadai da wannan hukunci.
Tace babu abinda mutum zai fada da ya kamata ace an yanke masa hukuncin kisa. Tace yanke hukuncin kisa saboda batanci take hakkin bil’adama ne da kuma gwamnati ya kamata ta hana aiwatar dashi, kamar yanda ta bayyana a shafinta na Twitter.
Ta ci gaba da cewa wadannan jihohi fa sune suka ki yankewa mayakan Boko Haram da suka kashe mutane hukuncin kisa,kamar yanda hutudole ya fahimta, inda ta kuma kara da cewa abinda ya kamata a yi shine a aikewa mawakin da wasika cewa abinda ya fada bai kamata ba amma ba hukuncin kisa ba.