Rahotanni

Yankin Yarabawa Ne Mafakar Duk Wani Dan Najeriyan Da Masifa Ta Koreshi Daga Gidansa, Inji Olu Fale..

Spread the love

Yarbawa Sun Kashe Makudan Kudade Da Yawa Don Tabbatar Da Zaman Lafiya A Najeriya, Inji Dattijon Yarabawa Olu Fale…

Dattijo Cif Olu Falae, ya ce Yariman Yarbawa ne ke hada Najeriya baki daya.

Ya ce al’ummar Yarbawa sun kashe kudade da yawa don tabbatar da zaman lafiya a kasarnan don haka, ba za a yi maganar rabuwar kai ba.

Falae, wanda tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya ne, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Vanguard, inda yake cewa idan rashin tsaro ko rikici ya bar ‘yan Najeriya, yawanci suna samun kwanciyar hankali ne a yankin Kudu Maso Yamma.

Ya bayyana kasar Yarbawa a matsayin “sansanin ‘yan gudun hijirar Najeriya … inda ake karban kowa da kulawa.” MediaOlu FalaeSahara Reporters Media Ya ce, “Mun sanya hannun jari, watakila, fiye da mafi yawan kungiyoyin a Nijeriya.

Idan akwai rikici a Gabas a yau, ina mutane suke gudu? Kudu maso Yamma. Idan akwai rikici a Arewa, to ina suke gudu zuwa? Kudu maso Yamma. “Wannan sansanin yan gudun hijirar Najeriya ne.

Nan ne ake maraba da kowa, ake karbarsa da kulawa.

Wannan shine saka hannun jarin zaman lafiya da muke samu tun daga lokacin tunawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button